A wani rahoto daga sashen Fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Mawlawi Ruhul-Amin, wani masani kan harkokin Musulunci kuma shugaban Cibiyar IMAE ta Indiya, a wani taron «Zaman Lafiya na Duniya da Tsarin Adalci na Kasa da Kasa», ya bayyana cewa: "A wannan lokacin da duniya ke fuskantar manyan matsaloli, gasa ta neman mulkin mallaka, da rashin tsaro mai yawa, salon jagoranci da kuma hangen nesa na Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei ya zama misali na musamman na siyasa da ke dogara ga 'yancin kai, neman adalci, da kuma gwagwarmayar fuskantar mulkin mallaka. Wannan shi ne wani tsari da zai iya zama jagora ga kokarin duniya na kafa zaman lafiya mai dorewa."
Ruhul-Amin, yayin da yake bayyana ra'ayoyin sa, ya yi nuni ga wasu muhimman abubuwa guda hudu:
Na Farko: Jagorancin Raya Al'adun Al'umma
Ruhul-Amin, a ci gaba da jawabin sa, yana mai ishara ga yaduwar tasirin al'adun yamma a duniya, ya jaddada cewa tsayawar Jamhuriyar Musulunci ta Iran wajen kare dabi'un Musulunci da kuma asalin al'ummar kasar, wata alama ce mai muhimmanci ga dukkan al'ummun masu neman 'yanci, kuma ta nuna cewa yana yiwuwa a kiyaye asali na al'adu da addini a gaban duniyar da ke fadadawa.
Na Biyu: Jagoranci wajen Neman Tsarin Adalci na Duniya
Ruhul-Amin ya ci gaba da cewa: "Ayatullah al-Uzma Khamenei, a fili ya yi jayayya da hanyoyin da manyan kasashe masu iko ke tafkawa ta kowacce fuska, kuma ya yi kira da a kafa wani tsari mai fadi na kasa da kasa da ke dogara ga adalci. Wannan salon, ana ganin shi a matsayin wajibi don cimma kwanciyar hankali da tsaro na duniya.
Na Uku: Falsafar Muƙawama, Alamar Girman Izza da Kuma Yarda da Kai na Kasa
Masanin na Musulunci, yayin da yake ishara da kalmomi kamar «Tattalin Arzikin Muƙawama» da kuma «Al'adar Muƙawama», ya ce wadannan hanyoyin, alama ce ta dogaro da kai, izzar kasa, da kuma jajircewar al'umma a gaban matsin lamba daga waje, kuma sana'a ce mai muhimmanci a tarihin zamani.
Na Hudu: Tallafawa Tattaunawa Tsakanin Al'adu
Ya bayyana muhimmancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wajen karfafa tattaunawa tsakanin addinai, al'adu, da kuma wayewar al'umma, ya kara da cewa wadannan kokarin sun ba da gudumawa mai muhimmanci wajen hada al'ummu da kuma rage tashin hankali na duniya.
Ya jaddada cewa duniya a yau fiye da kowane lokaci, tana bukatar jagorori da ke dogara kan adalci, ruhaniya, da kuma 'yancin kai, kuma ra'ayoyin da jagoran juyin musulunci suka gabatar za su iya bayyana hanyar cimma zaman lafiya da kuma rayuwa tare cikin lumana.
A ci gaba da jawabin sa, Ruhul-Amin ya yi ishara da ci gaban wannan salon a tarihi, inda ya jaddada cewa jagorancin Ayatullah al-Uzma Khamenei, ya kamata a dauke shi a matsayin ci gaba ta halitta ta ilimi da kuma gadon juyin juya halin Musulunci na Imam Khomeini (RA). Sannan kuma, sadaukarwa ga tallafawa kasashen da ake zalunta, fada a fili yayin fuskantar mulkin mallaka, da hada ruhaniya da kuma siyasa, su ne manyan abubuwa guda uku da suka sanya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama jagora ta musamman kuma mai tasiri a fagen kasa da kasa.
Ya kara da cewa: "Wannan ci gaban tunani da kuma aiki ya nuna cewa juyin juya halin Musulunci ba kawai wani abu ne na tarihi ba, a'a, ci gaba ne mai rai da kuma kuzari wanda ta hanyar jagoranci na yanzu, ya shiga wani sabon mataki kuma ya fadada, kuma ya samu ya zama tushen kwarai ga al'ummomi da dama a duniya.
Matsayi A Duniyar Zamani
Ruhul-Amin, yayin da yake ishara ga yanayi mai rikitarwa da kuma tashin hankali na duniyar yau wacce ke cike da yaki, gasa ta siyasa, da kuma matsaloli mabambanta, ya bayyana cewa salon Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karkashin jagorancin Ayatullah Khamenei, ya nuna jajircewa ga zaman lafiya, tattaunawa, da kuma adalci a harkokin kasa da kasa. Kuma kare hakkin kasashe masu rauni da kuma kokarin kafa dangantaka mai adalci tsakanin kasashe, zai ba da gudumawa mai yawa a tarihin zamani.
Ya bayyana cewa: "Tallafawa kasashe da ke karkashin matsin lamba da kuma jaddada adalci a harkokin duniya, ba wai kawai matsayi ne na siyasa ba, a'a, nauyi ne na dabi'a da kuma na dan'adam wanda zai iya tasiri wajen kafa makomar tsarin duniya."
Sababbin Hanyoyin Haske a cikin Tunani na Zaman Lafiya da Adalci
Masanin na Musulunci ya bayyana a karshe cewa wannan ra'ayi, ya bude sabon haske a cikin muhawara da ta shafi zaman lafiya na duniya, adalci na kasa da kasa, da kuma kiyaye asalin al'adu. Kuma jagoranci da ke dogara ga karfin ruhaniya, jajircewar dabi'a, da kuma adalci, zai iya fuskantar dukkan tarzoma, tashin hankalin duniya da kuma samar da abin koyi na ilimi da tabbatar da zaman lafiya. Wannan tunanin, ya fi ƙarfin a ce masa kawai ba siyasa, tsari ne na falsafa da akhlaq domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a duniya.
Your Comment